Wednesday

Home Sojoji Sun Lakadawa dalibai da malamai duka a wata Jami'a
Da Farko dai Sojojin sun shigo jami'ar ne suka dinga
suburbudan dalibai da malaman jami'ar.


A yanzu haka jaridar Punch ta samu rahoton
kulle jami’ar Osun biyo bayan wani
arangama da akayi tsakanin malaman jami’a
da daliban jami’ar da jami’an sojoji.

Lamarin ya auku a ranar talata 23 ga watan Mayu,
wanda yayi sanadiyyar mahukunta
makarantar kulle jami’ar.


labarai,sojoji,suburbudawani dalibi kenan bayan ya sha lafta.


“Shugaban hukumar jami’ar ya bada umarnin
kulle jami’ar har na tsawon sati guda, kuamya
shawarci dalibai da kowa ya koma gida daga
yau 23 ga watan Mayu. Kulle makarantar ya
ta’allaka ne ga afka ma jami’ar da wasu
jami’an sojojin sama suka yi, tare da jima
dalibai da malamai raunuka. Ana sa ran bude
makarantar a ranar 31 ga watan Mayu.”
Inji
sanarwar daga hukumar jami’ar UNIOSUN.

Hausa, arewa,lafta,hausapost28Ga wata daliba nan a kwance bayan ta sha suburbuda


Jaridar NAIJ.com ta ruwaito cewar jami’an tsaron da
aka jibge a jami’ar ne suka afka cikin jami’ar
dauke da makamai da motocin yaki da niyyar
kama wasu dalibai da ake zarginsu da aikata
sata irin na shafukan yanar gizo.

A yayin arangamar, an jikkata dalibai 11 da
ma’aikatan makarantar su 2, an ruwairo
sojojin sun kai harin mai kan uwa da wabi ne
a cikin jami’ar.

Da yake tabbatar da rikicin, shugaban sashin
kula da walwalar dalibai na jami’ar Dr
Adebimpe Adigun yace “Abin ba kyawun
gani, yanzu haka daliban mu 6 suna asibiti an
kwantar dasu, 5 kuma basu samu gado ba,
haka zalika malamai guda 2 sun jikkata
sakamakon harin Sojojin.”
No comments:
Write Comments