Tuesday

Home Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta tafi birnin Landan a yau Talata, Don Ganin Mijinta
Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta tafi birnin Landan a ranar Talata, 30 ga watan Mayu, kwanaki 23 bayan mijinta ya bar kasar domin ci gaba da jinya.

 A cikin wani jawabi dauke da hotunan uwargidan shugaba Buhari a lokacin da ta isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, mataimakiyarta ta musamman a kafofin watsa labarai, Adebisi Olumide Ajayi ta ce ta tafi birnin Landan ne domin kasancewa da mijinta na dan wani lokaci.

 Jawabin ya zo kamar haka: “Mai girma uwargidan shugaban kasa zata dauki tsawon wani lokaci tare da minjinta shugaba Muhammadu Buhari wanda a yanzu ya ke hutun jinya.
Uwargidan Buhari ta nuna godiyarta ga miliyoyin ‘yan Najeriya dake ta yima maigidanta addu’an samun lafiya da kuma fatan dawowa lafiya.”

 
NAIJ.com ta rawaito cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi birnin Landan don ci gaba da jinya a ranar 7 ga watan Mayu. 

Uwargidan shugaban kasa Buhari ta mayar da hankali ga aiki da take kaddamarwa a yankin Arewa maso gabas, don ganin ta tallafa wa mata da sana’oi, karatun yara mata da kuma bayar da cikakken kula ga yan gudun hijira a Arewa maso gabas.
No comments:
Write Comments