Wednesday

Home Allahu Akbar! Tsohon Gwamnan Jihar Taraba Danbaba suntai Ya Rasu.
An ruwaito cewar ya shiga wani yanayi tun
bayan afkuwar hatsarin na jirgin sama
Mista Danbaba Suntai, tsohon gwamnan jihar Taraba, ya mutu.

danbaba suntai


Gwamna Danbaba Suntai ya samu mummunan
rauni a lokacin da jirgin sa ya fadi a ranar 25 ga watan Oktoba, 2012 a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Ya samu tabuwar hankali tun bayan hatsarin kuma a yanzu an tabbatar da mutuwar sa a kasar Amurka.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Suntai ya shiga wani yanayi tun bayan afkuwar hatsarin na jirgin sama a ranar 25 ga watan Oktoba, 2012 a jihar Adamawa.

Mista Emmanuel Bello wani tsohon
kwamishinan labarai a jihar, ya tabbatar da mutuwar tsohon gwamnan a Abuja a ranar
Laraba.

Bello, wanda ya yi aiki lokacin Suntai, ya ce,
“tsohon gwamna ya mutu a kasar Amurka.”
No comments:
Write Comments