Friday

Home Ko Kasan Dalilin Da Yasa Shugaban Nigeria Muhd Buhari Ya Zabi Asibiti A Landan Don Kula Da Lafiyarsa??

Ministan ya ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa shugaban kasa Buhari na hannun kwararru a birnin Landan.

laimuhammed,buhari,asibitin landan

    Ministan bayanai da al’adu, Lai Mohammed ya yi bayani kan dalilin da ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fi son tafiya birnin Landan don samun kulawa da lafiyarsa, yayinda ya yi burus da asibitocin Najeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Lai
Mohammed ya ba da bayanin a lokacin wani
shiri na gidan radiyo mai taken , ‘Morning
Crossfire’, a tashar Nigeria Info Abuja
95.1FM, a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni.
A lokacin shirin wani fusataccen mutun ya
soki gwamnatin APC da ta saba ma
alkawarinta da hana jami’an gwamnati tafiya kasar waje domin duba lafiyarsu.

Lai Mohammed ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari na bukatar kulawa mafi inganci ta fannin lafiya.

A yayinda ya ke maida martani, Mohammed
ya ce shugaban kasar ya tafi neman magani a kasar waje ne saboda ya na bukatar kulawa ta musamman.“Amsa na mai sauki ne sosai. Shugaban kasar
mahaifinmu ne, shine jagoran kasar sannan
kuma a gani na ya cancanci kulawar mafi
inganci ta fannin lafiya."


A halin da ake ciki, gwamnatin tarayya ta ba
yan Najeriya tabbacin cewa shugaban kasa
Muhammadu Buhari na hannun kwararru a
birnin Landan.
No comments:
Write Comments