Thursday

Home Kowa yaje ya mallaki katin zama dan kaduna :inji Nasir el-rufai
Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da fara yin rijistar ga duk wani mazaunin jihar domin sanin iya adadin mutanen dake zama a cikinta.

katin zama dan kaduna,kowa,mallaki,kowa,nasir el rufai,gwamnan kadu a,kaduna


Kwamishinan Kasafin kudin Jihar,
Mohammed Abdullahi ne ya sanar da haka
ranar Laraba da ya ke nasa rijistan a
Kaduna.


Mohammed ya ce gwamnati ta fitar da haka
ne saboda ta san iya adadin mutanen da ke
zama a karkashinta sannan kuma ta iya
wadata al’umman da ababen more rayuwa.
Gwamnati ta umurci duk wani wanda zai
zauna a jihar da zai kai kwanaki 180 da ya tabbata yayi wannan rijista.
Ya ce: “wasu daga cikin dalilan yin wannan rijista shine domin gwamnati ta iya samarwa mutane ababen more rayuwa da kuma kara samar da tsaro a jihar.”

Ya kara da cewa gwamnati na shirin samar
wa mutanen jihar ababen more rayuwa
wanda sai mutum yana da wannan shaida ne
za iya amfana da wasu da ga cikin su.
Ya ce mutane su ziyarci wuraren da
gwamnati ta kirkiro domin yin rijistan ko
kuma a je ma’aikatar samarda da katin
shaidan zama dan kasa domin a yi rijista.

No comments:
Write Comments