Saturday

Home Lai Muhammed | Dalilin Da yasa Gwamnatinmu Bata Bin Umarnin Kotu.
A zaman taunawa da yake da wata kafar
jarida a Abuja, Ministan yada al'adu da
labarai na kasa, Alh. Lai Mohammed, yace a matsayinsa na lauya, ya san dole ya girmama kotu, kuma ya fahimci karfinta, amma yasan ba komai suka gama sani ba a batun wadanda ake tuhuma, don hakahukuncinsu
gurdadde ne.

dalilin,umarnin kotu,gwamnatin,buhari

  • "Dole ne mu dubi hakkin zaman lafiyar
    al'umma kafin mu dubi hakkokin ram mam men £}}
    mutum daya, su masu bada hukuncin basu da
    faffadar masaniya game da illar wadanda
    muke zarga" , inji shi.

Yana dai bayani ne kan batun kin sako
tsohon mai baiwa shugaba Goodluck Jonathan
shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo
Dasuki, da kuma shugaban kungiyar
musulman shi'a masu biyayya ga kasar Iran,
Malam Ibrahim El-Zazzaki na Zariya,
wadanda aka kama su shekaru biyu da suka
gabata aka kuma ki sako su duk da umarnin
kotu na ayi hakan.
<br />
Ana dai zargin gwamnatin Buhari da kin
girmama doka da biris da take hakkokin dan-adam, zaarin da ministan ya musanta.

"Ya zaka zarge mu da mulkin kama karya?
bayan nima Lauya ne, na kuma san aikin kotu, na kuma san ilolin wadannan talikai? gwamnati ta fi kotuna sanin bayanan sirri a kan wadannan mutane, don haka ake ajje dasu har yanzu"
, ya kara da cewa.

Ana dai tuhumar Sambo Dasuki da wawaso
da kasa kudin kasa ga mukarraban
gwamnati, da ma handama. Shi kuma El-
Zazzaki ana tuhumarsa da ta'addanci da cin amanar kasa.

Source : Naij.com Hausa
No comments:
Write Comments