Friday

Home Tashin Bom Yayi Sanadiyyar Kashe Yara Biyu : Adamawa
A daren jiya Alhamis ne aka samu tashin wani bam da ya kashe wasu kananan yara biyu ya kuma jikkata wasu a unguwar Fadaman Rake dake garin Hong a jihar Adamawa.

      boko haram,ayyukan ta'addanci,bom,adamawa,yola

Rahotanni dai na nuni da cewa wani direba ne dake tuka wata karamar mota kirar starlet, ‘dauke da bam din cikin bakar leda, inda nan take ya samu
wasu yara dake bakin titi suna wasa a nan
ne ya yaudaresu da cewa wai sako ne aka
bashi ya baiwa baban wani yaro.

Bayan da yaran suka karbi ledar da zummar
zasu kai gida, tafiyar direban ke da wuya
bam din ya fashe kafin su karasa gida.

Nan take ya kashe yara biyu wasu kuma suka
raunata, inda aka garzaya da su asibiti.
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawan ta
bakin kakakinta SP Othman Abubakar, ta
tabbatar da faruwan lamarin.
Ya zuwa yanzu dai babu wani ko wata
kungiya data dau alhakin tashin bam din,

sai dai kuma wannan na zuwa ne yayin da
hukumomin tsaro ke gargadin cewa bayanai
na nuni da cewa ‘yan ta’adda yanzu na
sauya salo, don haka ake gargadin jama’a da akula, musamman a wuraren hada hadar
jama’a da kuma wuraren ibada, kamar
yadda kakakin rundunan yan sandan yayi
Karin haske.

Yankin Hong dai na daga cikin yankunan da
a baya suka fada hannun mayakan Boko
Haram, kafin daga baya dakarun Najeriya
bisa tallafin yan sakai suka kwato yankin, wanda kuma tun wancan lokaci ba’a sake jin wani abu ba sai yanzu.

Source :Voa hausa
No comments:
Write Comments