Thursday

Home Za’a ƙKaddamar da dokoki guda 9 da zasu hana shan sigari a Najeriya.



Ministan kula da kiwon lafiya, Isaac Adewole
ya sanar da wasu dokoki guda tara wadanda
gwamnati zata fara kaddamarwa domin rage
ta’ammali da sigari a Najeriya, kamar yadda
Premium Times ta ruwaito.


hana shan sigari a Nigeria


Ministan ya bayyana dokokin guda tara da
suna ‘National Tobacco Act’ wanda yace
tsohon shugaban kasa Jonathan ne ya rattafa
hannu akan dokokin tun a shekarar 2015,
amma ba’a kaddamar ba.


Ministan ya bayyana ma majiyar NAIJ.com an
samu tsaiko wajen kaddamar da dokoin
sakamakon wasu karin tsare tsare da ake
bukatar majalisa ta sanya hannu akai.


hana shan taba a Nigeria

Ga dai jerin dokokin nan, guda 9:



1- Hana siya da siyarwar Sigari ga duk
wanda bai kai shekaru 18 ba.

2- hana siyar da Sigari guda daya, sai dai
guda 20.

3- Ba za’a siyar da Sigari mara hayaki ba har
sai ya kai gram 30.

4- Hana cinikayyar siya da siyawar Sigari a
shafukan yanar gizo.

5- Dakatar da kamfanunuwan Sigari daga
shiga harkar Lafiya.

6- Hana busa Sigari a bainar Jama’a, ko duk
inda jama’a ke taruwa kamar su makaranta,
Asibiti, wajen wasan yara, wajen shakatawa,
manyan shaguna, filin wasanni, dakunan cin
abinci da sauransu.

7- Kamawa da gurfanar da duk mutumin
daya mallaki ireiren wuraren da aka ambata,
kuma ya bari aka sha Sigari a cikinsu.

8- Hana tallar Sigari da kawayenta

9- Tabbatar da an bi tsare tsaren da suka
dace wajen hada Sigarin.

(source: Naij.com hausa)
No comments:
Write Comments