Wednesday

Home Abin da yasa Nnamdi kanu yayi kaurin suna a gwamnatin buhari:


Daya daga cikin manyan Matasan Arewa da
su ka cewa Inyamurai su bar Yankin Shettima
Yerima yace tun farko bai dace Gwamnatin
kasar ace ta kula jagoran Kungiyar IPOB
Nnamdi Kanu ba.


Shettima Yerima yayi kaca-kaca da Nnamdi Kanu
Yerima yake cewa da can Nnamdi Kanu
karamin alhaki ne amma yanzu yana nema
ya gagari har Gwamnonin Yankin da sauran
manyan sa don kuwa sun rasa yadda za su yi
da shi. Shi dai wannan mutumi yace ba za su
zura idanu ba kurum a matsayin su na 'Yan
Najeriya.

Alhaji Yerima yace kaman shi da aka yi ne
har aka tsare sa ya fara ba shi dama ya zama
abin da ya zama watau Nnamdi Kanu. A baya
kun ji Yerima ya kira wannan Matashin da
wanda yake shan miyagun kwayoyi.
Kwanki kun ji Mutanen Jihar Ribas da
Benuwe sun ja kunnen jagoran Kungiyar
IPOB ta Biyafara watau Nnamdi Kanu inda su
kace idan yana haukan sa ya daina hadawa
da su.

(Naij Hausa)
No comments:
Write Comments