Tuesday

Home ATIKU YA HALARCI TARON JAM'IYA MAI MULKI A KASAR INGILA KUMA YA ZIYARCI BUHARI.
ATIKU YA HALARCI TARON JAM'IYA MAI MULKI A KASAR INGILA KUMA YA ZIYARCI BUHARI.

Usama jaafar comrade

Tsohon mataimakin shugaban
kasa Alhaji Atiku Abubakar ya
samu ganawa da Firami Ministan
kasar Birtaniya, Uwargida Theresa
May a yayin taron jam’iyyar
Conservative na kasar.

Wannan bayani ya fito ne daga
bakin Atikun kansa, inda ya
bayyana haka a shafinsa na kafar
sadarwar zamani, Tuwita.

A yayin taron walimar, Atiku ya
sake yin watan ganawa da dan
majalisar dokokin kasar Birtaniya,
Liam Fox, kamar yadda ya shaida
a shafin nasa na Tuwita.
Atiku tare da Firai Ministan
Birtaniya Sa’annan Atiku Abubakar ya samu rakiyar dan majalisar dattawan najeriya Mr. Ben Murray Bruce, wanda tare da shi suka halarci wannan muhimmin taro.
A karshe Atiku yace sun ziyarci maigirma Shugaban kasar najeriya
Mal. Muhammadu Buhari Atikun ya yaba a halin da yasami Buhari kuma yace hakika wasu zasuji kunya akan yadda suke ruruta jikin Buharin alhali kuma ba haka bane.
Kuma yace Tabbas buhari zai iya gudanar da gwamnatinsa a najeriya ko a gobe ya dawo.
Kuma ya kara Rokan al'ummar najeriya cewa Ko kogi baiki kari ba, don haka shugabannin addinai da mabiya su taimakawa Shugaban namu da Addu'ar neman sauki.

No comments:
Write Comments