Sunday

Home Bayan Sana'ar Man Fetur Babu Sana'ar Da Ta Kai Film Samun Kudi Cewar Adam A. Zango
Fitaccen jarumin fina-finan Hausan nan Adam A Zango ya bayyana cewa, banda sana'ar man fetur, ba sana'ar da ta kai sana'ar fim samun kudi.

Adam A Zango ya bayyana haka ne, a zantawarsa da Gidan Rediyon BBC.

Jarumin ya kara da cewa fim din Gwaska na daga cikin fina-finan da ya samu kudade a dukkanin fina-finnan da ya aiwatar, Kana ya bayyana wakar "Gumbar Dutse" a matsayin wakar dake zama bakadamiyar sa daga cikin wakokinsa.
No comments:
Write Comments