Tuesday

Home Bukola Saraki ya bayyana babban abin da ke ci wa Gwamnatin Buhari tuwo a kwarya.
- Sanatocin kasar nan sun ce fasa kaurin da ake
yi a Najeriya yayi yawa matuka
- Kwamitin Majalisar tace kayan da ake shigo da
su a sace sun wuce na Tiriliyan 7
Shugaban kwamitin da ke kula da harkar
shigo da kaya cikin Najeriya a Majalisar
Dattawa Sanata Hope Uzodinma ya koka da
yadda ake shigo da kaya ta barauniyar hanya
cikin kasar.Majalisar tace Bankin Duniya ya bayyana
cewa kayan da ake fasa kaurin su a Najeriya
sun haura Tiriliyan 7 a kowace shekara
wanda ya zarce kasafin kudin kasar. Bukola
Saraki yace idan har ana so ayi matsalar
tattalin arzikin dole a shawo kan wannan
matsala.

Saraki ya bayyana babban matsalar Gwamnatin APC
Shugaban Majalisar Dattawan kasar nan
Bukola Saraki yace muddin Hamid Ali yayi
maganin harkar fasa-kauri a Najeriya to ya
sa duk tufafin da ya ga dama ko wandon
turoza ne da 'yar fikikiyar riga ko ma wane
iri. Saraki yace shi zai ma mara masa baya a
kan wannan kudiri.

Daga :Naij.com Hausa
No comments:
Write Comments