Tuesday

Home Dalilin Da Yasa Na Sauka Daga Mukamina :Kabiru Alasan Rurum
Shugaban majalisar dokokin Jihar Kano,
Alhaji Kabiru Rurum, a ranar Litinin, 3 ga
watan Yuli yayi murabus biyo bayan zargin
da aka yi masa na karbar cin hancin naira
miliyan 100 daga hannun attajiri nan Alhaji
Aliko Dangote domin majalisar ta yi watsi da
binciken da ake yiwa sarkin Kano Alhaji
Muhammad Sanusi II.


majalissa, dokoki, jihar kano, dalilin
Tsohon shugaban majalisar dokokin Jihar Kano, Alhaji
Kabiru Rurum


Rurum ya rubuta wasikar sauka daga
mukaminsa wanda mataimakin shugaban
majalisar, Ibrahim Chidariof ya karanta a
lokacin zaman majalisan na musamma
saboda zargin karbar cin hanci akan
binciken da majalisar ta ke yiwa sarkin Kano.
Ana zargin tsohon kakakin majalisar ne da
karba cin hancin naira miliyan 100, amma
ya kasa raba kudin da sauran ‘yan majalisar.

Tun da farko, a wani jawabinsa a gaban
majalisar dokokin kafin su tafi hutun Sallah,
tsohon kakakin ya musanta zargin yayin da
kuma ya yi barazanar kai karar kamfanin da
ta watsa labarin.

Kamar yadda muka samu labari,
mataimakin shugaban majalisar, wanda ya
karanta wasikar ya ce Rurum ya yi murabus
ne don kare martabarsa saboda zargin cin
hanci da rashawa da ‘yan majalisar ke masa.
Tuni 'yan majalisar suka amince da wasikar
tsohon shugaban majalisar na yin murabus
suka kuma maye gurbinsa da Honarebul
Abdullahi Ata a matsayin sabon shugaba.
Sabon shugaban ya yi alkawarin tafiya da
kowa domin a kawo cigaban majalisar.
No comments:
Write Comments