Sunday

Home Hankalin yan majalisa ya tashi : Wasu kasashe 25 sun marawa Magu baya (katanta)
Wasu kasashe 25 sun marawa Magu baya a yaki da cin hanci da yakeyi....

Magu_EFCC


Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, Ibrahim Magu ya samu goyon baya daga kasashe 25 da suka yi na'am da kokarin da yake yi na yakar cin hanci da rashawa a Nigeria.A wani zaben jin ra'ayoyin jama'a da kungiyar wanzar da zaman lafiya ta duniya "Global Peace Movement International" ta gudanar ya nuna kasashen duniya sun gamsu da shugabancin hukumar EFCC da ayyukan ita kanta hukumar.

Hausa times ta ruwaito shugaban Global Peace Movement International din, Dr Mike Uyi, yana bayyana cewa Mista Magu ya lashe kashi mafi rinjaye (96%) a kasashen Amurka, da Ingila da Fransa, da Germany, da Russia, da Canada, da Chinada kuma BelgiumSai dai a yayin da duniya ke yabawa tare da kwaikwayon kwazonsa, anan Nigeria har yanzu yan majalisar tarayya sun ki tantance shi a matsayin shugaban EFCCYa kuke kallon wannan lamari?
No comments:
Write Comments