Sunday

Home Inã Masu Sha Awar Fitowa a Fim Din Hausa To Albishirinku Ga Dama Tasamu (Karanta)

Albishiri Ga Masu Sha Awar Fitowa a Fim Din Hausa Ga Dama Tasamu (Karanta)Ko Kuna Da Labarin Sabon Shirin “GISHIRIN RAYUWA”?

A karon farko farfajiyar shirya finafinan Hausa wadda aka fi sani da Kannywood za su dibi mutanen gari dake da sha’awar fitowa a fim cikin sabon shirin wasan kwaikwayo da za’a fara dauka kwanan nan.

Shirin mai suna “GISHIRIN RAYUWA” zai maida hankali ne fannin ilimantarwa da nishadantarwa da fadakarwa, kuma zai bambanta da yadda aka saba shirya sauran fina-finai.

Yanzu haka dai an bude kofa ga duk mai sha’awar shiga ko fitowa a cikin sabon shirin wasan kwaikwayon.

Duk mai sha’awa zai je kai tsaye ayi masa gwaji domin tantancewa kamar haka:-

A Jihar Kano


Za’a yi taron tantance yan wasan

 • A Ranar Asabar da Lahadi, 22 da 23/07/2017

 • Waje: Dankin Taro Na Mumbayya Housedake Gwammaja Kano.

 • Lokaci: Da Karfe 9:00 na safe

 • Domin karin bayani sai a tuntubi lambar waya 0703 883 8890

A Garin JOS


Za’a yi taron tantance yan wasan ne kamar haka:-

 • A ranar Asabar da Lahadi 29 da 30/07/2017

 • Waje: Mega Park dake kan titin Bauchi, Bauchi ring road, Jos

 • Lokaci: Da karfe 9:00 na safe


  Marubutan shirin (Writers)

 • Nazir Adam Salihi
 • Nasir NidNazir Alkanawi

 1. Shiryawa (Producer):- Ahmed Muhammed Sarari.

 2. Mai bada umurni (Director):- Falalu Dorayi.

Kamfanin SKM tare da hadin guiwar Kannywood Entertainment ne suka dauki nauyin shirin.

Domin karin bayani sai a tuntubi: Lambarwaya 07038838890 Zamu cigaba da kawo maku rahoton yadda ta kaya a wajen tantancewar.
No comments:
Write Comments