Sunday

Home Kadan Daga cikin Sharrukan sanya security code a wayoyin mu | karanta ko ka fadaka
SANYA PASSWORD A WAYA YAKAN IYA ZAMA SHIRIRITA WAI ZANI DA ALJIHU.
sanyawa waya password
  • Abokai uku sukayi hatsari a mota duk suka jikkata. Saiga wani mutum yakawo musu agaji yana neman yakira wanda zai kawo dauki. Ga wayoyi guda 6 motar ammana kowacce da password dinta. Sanadiyyar hakan suka rasa rayukansu.
  • Wata mai ciki ta fadi kasa sumammiya a gidan babu kowa sai wata yarta karama wacce batada waya. Yarinyar batasan meke faruwa ba tadai ga mahaifiyarta tana numfasawa da kyar. Tadauki wayar mahaifiyartan don ta kira mahaifinta, ammana wayar akwai password. Sai akayi sa'a wani yayanta yabar wayarsa a kan gado yatafi makaranta domin anhansu xuwa da phone makaranta. Tadauka ta kira mahaifintan cikin ikon Allah aka ceto rayuwarta saboda wayar yayanta (danta) babu password. Da ace ta rasa ranta da laifin waye?.
  • Wassu yanfashi suka je fashi wani gida. Wani yaron gidan yana wani karamin daki wanda yanfashin suka zata store NE basu shigaba. Yaron bashida waya, sai kuma yazamana ga wayar Abbansa a dakin tana caji. Yayi kokarin Kira domin a kawo musu agaji ammana wayar akwai password. Sukayiwa yanmatan gidan fyade suka kashe su duk, sukabar wannan yaron Shi kadai domin basu ganshi ba. Duk abinda yake faruwa yana gani ta window. Kusa dasu kuwa akwai police station ga kuma army barrack ma ba nisa dasu kuma duk yanada numbers din ammana babu yadda zaiyi domin wayar Addan nashi akwai password.
  • Wani matashi ya mutu wanda yakeda wassu maqudan kudi a wani banki. Duk bayanan suna wayarsa. Ammana babu wanda zai iya gano bayanan saboda wayar tashi akwai password. Shawara gareku Yan'uwa masu hankali da tunani: Kimar ka/ki yafi daraja sama da bayanan da kake/ kike kokarin 6oyewa. Idan yazama dole zaka/zaki 6oye sirrin, yazama password din a whatsapp, text messages, facebook, files, da sauransu za a sanya sai a bar wajen yin kira a bayyane babu password domin tayiyu watarana ka ceci rayuwarka ko rayuwar na Kusa dakai.
Idan banda duniya wayan rashin gaskiya tayi yawa banga abinda zaisa Gaye daga yayi aure saikaga pattern din wayarsa takara tsayi. Mai hankali shike gane dingishin kwado a ruwa. Allah Yasa mu fadaka baki daya. YASEER GOMBE
No comments:
Write Comments