Monday

Home LABARI DA DUMIMI DAGA MAJALISSAR JIHAR KANO

New speaker


Shugaban majalissar jihar kano Hon. kabiru alhasan rurum ya yi murabus daga mukamin sa na kakakin majalissar jihar kano.


"yan majalissar dai tun a baya sunyi kokarin sauke shi inda yan majalissu sama da talatin 30 suka rattaba hannu a kan takardar tsigewar.


Bayan yayi murabus a yau, A take Aka maye gurbin sa da hon. yusuf Abdullahi ata.

Hon. kabiru Alhasan rurum yana cikin majalissar lokacin da akayi sabon nadin har aka kammala.

An samu sauye sauye da dama a majalissar ayau.


Yusuf Abdullahi Ata shine shugaban masu rinjaye na majalissar inda bayan rantsar dashi a take aka maye gurbin sa da hon. Abdul-aziz garba gafasa a matsayin shugaban masu rinjaye.


kujerar mataimakin shugaban masu rinjaye itama anyi gaba da ita, inda aka sutale Mai fada Bello kibiya aka maye gurbinta da wani dan majalisssa.

Yanzu an kafa wani kwamitin karkashin bulaliyar majlissa Abdul madari da sauran membobinsa guda 6 da zai gudanar da bincike a majalissar inda aka basu tsawon wata uku.

wannan takaitaccen rahotone kubiyo mu a posting dinmu na gaba don jin cikakken rahoton.
No comments:
Write Comments