Tuesday

Home More Picture's : A karon farko an daura auren wasu kattin maza su biyu masu ikirarin su Musulmi ne a kasar Ingila.

A karon farko an daura auren wasu kattin maza su biyu masu ikirarin su Musulmi ne a kasar Ingila.

Jahed Choudhury dan shekara 24 ya angwance da abokin Luwadinsa Sean Rogan mai shekara 19 a sigar auren Musulunci a kotun daura aure dake Walsall

Hausa times ta ruwaito yan luwadin Biyu sun kasance tare tsawon shekaru Biyu, Bayanai sunce soyayya ta kullu ne tsakanin yan Luwadin a lokacinda Sean ya yi kicibis da matashi Choudhury na kuka cike da damuwa zaune a akan wani Benci a garin Darlaston.

Bayan mista Sean ya lallashi matashin ya bashi gagarumin taimako daga nan sai ya cigaba da yaudararsa ta hanyar bashi kulawa da kaytuttuka har ya koya masa Luwadi.

Duk da cewa iyaye da yan'uwan Choudhury sun kauracewa wannan fasikanci tare da Allah wadai kuma suka ki halartar auren amma hakan bai damu matashin ba domin a cewarsa "Sean yayi masa gata a lokacinda yake cikin matsananciyar damuwa"

Suna masu bayyana cewa sunyi farinciki da auren junansu da sukayi musamman ganin cewa su Musulmu ne domin yin hakan zai nunawa duniya cewa musulunci bai hanasu cika burinsu ba.No comments:
Write Comments