Friday

Home Wasu "Yan bindiga sun yi Awon gaba da manya-manyan makamai bayan sun hallaka wani jami'in soji:
"Yan bindigar sun raunata wani jami’in Sibil
Difens a harin.

Wasu 'yan bindiga a misali karfe 2 na dare a
ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli sun mamaye
dakaru da ke Ogbogbagbene a yankin
karamar hukumar Burutu a Jihar Delta, inda
suka kashe wani soja, yayin da suka jikkata
wasu jami’an, suka kuma yi awon gaba da
wasu manyan-manyan bindigogi.
‘Yan bindigar da ba san ko su wanene ba, sun
raunata wani jami’in Sibil Difens a harin.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun
rinjaye sojojin da ke bakin aiki a wannan
lokacin.
Kauyen Ogbogbagbene ne garinsu tsohon
ministan Neja Delta a gwamnatin da ta
gabata na tsohon shugaban kasar Gooduck
Jonathan, Dattijon Godsday Orubebe.
‘Yan bindigar da ba san ko su wanene ba
Kwamishinan 'yan sanda, na jihar Delta,
Mista Zanna Ibrahim, wanda ya tabbatar da
aukuwar lamarin ga Majiyar NAIJ.com , ya ce:

“ Wasu ‘yan bindigar da ba san ko su wanene
ba sun kai hari wani kauye a karamar
Hukumar Burutu, inda suka kashe wani soja
da kuma jikkata wasu”.

Ibrahim ya bayyana cewa, 'yan sanda
karkashin jagoranci wani babban jami'in'
yan sanda, DPO na Burutu sun sa idanu a
halin da ake ciki yanzu.
No comments:
Write Comments