Friday

Home Yanda Zaka Samu Rancen Kudi Har N100,000 A Layin Etisalat New(9mobile)

Katafaren kamfanin sadarwar nan na Etisalat da yanzu aka canzawa suna zuwa 9mobile sun fito da wani tsari da zai baiwa kwastomomin sa damar cin gajiyar wani tsari da zai rinka basu damar rantar kudi har Naira dubu dari (~N~100,000) zuwa abinda yayo kasa zuwa akawunt dinsu na banki don yin hidindimunsu na rayuwa dasu wanda zasu biya a can gaba.

Yanda Zaka Samu Rancen Kudi Har N100,000 A Layin Etisalat New(9mobile)
Idan baku manta ba ma kamfanin MTN tare da hadin gwuiwar Diamond bank suna da wannan tsari ta hanyar Diamon Y’hello account dake baiwa kwastomomin su damar karbar rancen kudi wanda daga bisani mutum kan biya.

To suma kamfanin na 9mobile sun yunkoro da wani tsari mai suna KwikCash dake baiwa mutane damar karbar rancen kudin.
Ba tare da dogon surutu ba bari nayi muku bayani kan yadda zaku samu wannan rance.

Daga : umar Alkalin fzbuk

Da farko dai sai mutum ya sami Layin Etisalat sannan sai yabi wadannan matakai:
  • – Da farko sai ku danna *561#
  • – Sai a zabi “Request loan”
  • – Wajen preferred loan offer sai a zabi Bank sannan sai mutum ya sanya lamabar akawunt dinshi ta banki(account number)
  • – Daga nan sai ka zabi gabi da tabbatar da yawan kudin da kake son ka ranta din, sannan sai ka karbi “terms and conditions” nasu sannan sai kayi submit..
Idan kana so ka biya bashi to sai ka danna *561#,sai ka shiga wajen Pay loan , sai kabi ragowar matakan sa zasu biyo baya.


Ku sani cewar: kowa na da damar cin moriyar wannan tsari, ma damar mutum na da layin Etisalat(9mobile) sabo ko tsoho..
No comments:
Write Comments