VISIT US ON AREWASOUND.COM


HOTTREND ONLINE :
Music Mp3 - Sabuwar Wakar Hamisu Breaker mai suna - Bazana Manta Maryam Ba.
CHECK NEW PRODUCTS HERE
Hamisu breaker 2020 Album Download Mp3 music

Sammani aa 2020 Album : Download Complete Album (Akwai lokaci)

Umar M Shareef Zeenaru 2020 Official AUDIO+VIDEO

MUSIC: Melery 2020 Song Da Dadi So

Wednesday

Home Yanzu-yanzu Sojojin Nigeria sun kashe "yan ta'adda har guda shida 6
Dakarun rundunar sojin Najeriya na
birgediya 7 tare da hadin gwiwar jami’an
tsaro na kar ta kwana sun yi nasarar
kakkabe ‘yan ta’adda dake zaune a kauyen
Dawashi Gari, a wani yanki da ke iyakar
tafkin Chadi da kasar Najeriya.An samu labarin ne a cikin wata sanarwa da
mataimakin jami’in hulda da jama’a na
rundunar soji, mukaddashin darakta kanal
Timothy Antigha ya fitar wanda ke cewa a
safiyar Talata 11 ga watan Yuli.
Dakarun sojin sun yi nasarar kashe ‘yan
ta’adda 4 a yayin da sauran suka gudu suka
bar baburan su wanda aka gano aka lalata.

Har ila yau, a duk cikin yunkurin da ake yi
wajen ganin an kawo karshen ta’addanci a
yankin arewa maso gabashin Najeriya, sojojin
bataliya 145 birged 5, da jami’an tsaro na kar
ta kwana sun samu nasaran barrantar
mayakan kungiyar ‘yan ta’adda daga kauyukan
Gashigar, Asaga, Bukarti da sauran kauyukan
da ke kusa da su.
Sun kwato wasu kayayyaki daga 'yan ta'addan
Hoto: Alummata
A wannan hali ne dakarun suka hadu da wasu
‘yan ta’adda a kauyen Kanama inda suka fafata
da su suka kashe 2 daga cikin sun sannan
kuma suka kama 2 tare da amshe makaman su
da baburan su.
No comments:
Write Comments