Saturday

Home › › An gano Alewa mai shekaru 100 a duniya {karanta kasha labari}
An gano alewa mai shekaru 100 a duniya
Wani mai bincike ya gano wata alewa mai shekaru 100 a Antatika, a inda ake tunanin alewar na wasu kungiyar turawane masu yawon bincike. Babban abin mamaki dai shine har yanzu kamshin alewar bata wani canja ba.Wani mai bincike ya gano wata alewa mai shekaru 100 a Antatika, a inda ake tunanin alewar na wasu kungiyar turawane masu yawon bincike. Babban abin mamaki dai shine har yanzu kamshin alewar bata wani canja ba.

An bayyana cewa wata kungiyar kare tarihin Antarctic sun zauna a yankin Cape Adare kimanin shekaru 100 da suka gabata, wadanda har yanzu akwai alamursu a gurin a inda aka samu alewa mai shekaru dari da kuma bata lalace ba.

An bayyana cewa ana tunanin kanfanin turawa mai suna Huntley & Palmers mai yin biskit ne ya kera alewar. Kamar dai yadda aka bayyana ana hasashen daya daga cikin 'yan yawon binciken Robert Falcon Scott ya kawo alewar a gurin a tsakanin 1910-1913 Alewar dake cikin wata kwali mai launar ruwar dorawa, duk da kwalin ya dan lalace, ita alewar tananan garas don launinta dama kamshinta bai canza ba.

Jagoran masu gudanar da nazarin a yankin Cape Adare dake Antactic Lizzie Meek ya bayyana cewa yayi mamaki kwarai da gaske ga irin yadda aka gano alewar mai shekaru hakka da yawa kuma bata lalace ba.

Za'a dai ajiye alewar a inda aka ganta bayan kammala nazari da ake gudanarwa.
No comments:
Write Comments