Friday

Home An gano me Abubakar Shekau ke son ya cimma da muguwar akidarsa.
Kungiyar Boko Haram ta dare gida biyu, ta kuma taba yi wa kungiyar ISIS ta Iraki mubayi'a, bayan da suka ga shugaba Buhari ya ci zabe,
kuma suka ji tsoron ko kashinsu ya bushe kenan.Shekau dai shine ke da Boko Haram, Sauran
kuma ISIL Wata kungiya mai adawa da ayyukan ta'addanci mai suna "Coalition against terrorism (CAT)" karkashin jagoranta, Shehu Garba, a taron da ta gudanar a kaduna ta ce shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, na kokari tukuru ya nuna wa masu daukar nauyinsa cewar har yanzu da ragowar karsashin kungiyar sa ta Boko haram duk da cewar a zahiri sojin Najeriya sun karya kashin bayan kungiyar.

Kungiyar ta "CAT" tana mayar da martani ne dangane da sabon faifan bidiyo da Abubakar Shekau ya saki da ya ke nuna tamkar kungiyar tasa na da karfi har yanzu, suna ma su bayyana cewa Shekau din na shure - shure ne kawai wanda ba ya hana mutuwa.

Shehu Garba ya ce 'duk wanda ya kalli faifan bidiyon zai shaida raunin shekau da kuma kokarin sa na aika sako ga masu daukar nauyin na sa domin samun sabuwar kwangila gabanin zaben 2019.'

Shehu Garba ya jaddada goyon bayan
kungiyar sa ga sojin Najeriya tare da basu karfin gwiwa a kan aniyar su ta cafke Shekau din cikin kwanakin 40 da hukumar sojin ta diba.

Shehu ya kara da kira ga 'yan Najeriya da su toshe duk wata kafa da kungiyar Boko Haram din ka iya amfani da ita wajen isar da sakon su ga masu daukan nauyin su ta hanyar kin yada faifan bidiyo ko hotunansu a dandalin sada zumunta nan zamani da ke yanar gizo.

Shehu yace 'gwamnatin Najeriya ya kamata ta tunkari kamfanunuwan yada labarai masu
matsuguni a yanar gizo domin toshe yada duk wani labari mai alaka da ta'addanci kamar yadda wasu kasashen duniya suka yi, idan kuma sun ki yin biyayya gwamnatin ta hana su damar yin kasuwanci a Najeriya.

A satin da ya wuce ne dai Shekau ya saki
faifan bidiyo yana yi wa shugaba Buhari da hafsan sojin Najeriya, Tukur Buratai,
shakiyanci kan umarnin da hukumar sojin ta bayar na kama shi cikin kwana 40.
Jama'a da dama dai da suka kalli faifan
bidiyon sun bayyana cewar shekau din na
yin karfi hali ne kawai domin a bayyane take cewar yanzu ya rasa kuzarin sa na baya alama da ke nuni da cewar a takure yake yanzu.

Watch This
No comments:
Write Comments