Sunday

Home An Kammala fitar da sunayen "yan takara 4 da zasu gaji shugaba buhari 2019:
Mun samu labari cewa a taron su IBB da Obasanjo da aka yi kwanan nan, an fitar da wasu 'Yan Arewa 2 da ake so
su gaji kujerar Shugaba. Buhari.Wadannan dai ba kowa bane sai tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanata a yana Rabiu Musa Kwankwaso da
kuma tsohon Kakakin Majalisar Wakilai kuma Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

Haka kuma akwai tsohon Gwamnan Jihar Kuros-Riba Donald Duke a lissafin. Na karshe kuma da aka kawo shine
tsohon Gwamnan Jihar Edo watau Adams Oshiomhole. Haka kuma manyan kasar su na kokarin ganin an samu
matashi a matsayin Shugaban kasar.

Jonathan Nda-Isiah na Jaridar Leadership ya kawo abubuwan da ke gaban Shugaba Buhari da zarar ya dawo gida yace akwai shirin sauya mukaman Gwamnati da kuma shawo kan matsalar tattalin arziki da Boko Haram.
No comments:
Write Comments