Thursday

Home APC TA YI WATSI DA KIRAN BUHARI YA SAUKA : KARANTA ABIN DA TACE.

A cigaba da cece ku cen da ya biyo bayan zanga-zangar bukatar Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus, APC ta yi watsi da wannan bukatar.

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi watsi da zanga-zangar nemar Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus saboda rashin lafiya. Jam’iyya ta yi nuni da yadda marigayi Shugaba Musa ‘Yar’adua na Jam’iyyar PDP shi ma ya jima ya na jinya. Ta ce ko ba komai ai Mukaddashin Shugaban kasa na aiki tamkar Shugaban kasa kuma kamar yadda doka ta tanada.

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, Alhaji Mustapha Salihu y ace cigaba da kasancewar Shugaba Muhammadu Buhari bisa gadon mulki na bisa ka’ida. Y ace babu ma shugaban kasar da ya kiyaye dokar Najeriya kamar Buhari.

Shi kuma wani tsohon dan Majalisar Wakilai daga jahar Nasarawa mai suna Ahmed Aliyu Wadata, ya jaddada cewa tunda akwai Mukaddashin Shugaban kasa an mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya. To amma wani dan jam’iyyar kuma mai suna Alhaji Adamu Bunuyadi y ace muddun Shugaba Buhari ya ga alamar ba zai iya cigaba ba, to abu mafi dacewa shi ne ya yi murabus.

WATCH VIDEO
(Voa hausa)
No comments:
Write Comments