Friday

Home Assha! Wani malamin islamiya a kotu bisa zargin lalata da daliban sa 3
Assha! Wani malamin islamiya a kotu
bisa zargin lalata da daliban sa 3

Wani al'amari mai kama da almara da kuma
tashin hankali ya afku a karamar hukumar Ikeja
ta jihar Legas inda iyayen wasu yan mata uku da
shekarun su bai haura sha biyu ba suka maka
malamin islamiyar su a kotu bisa zargin yin
lalata da.

Mahaifin yaran mai suna Clifford Ogu wanda
ya shigar da karar a gaban kotun ya
shaidawa alkalin cewa malamin ya aikata
wannan ta'asar ne tun daga watan Mayu har
zuwa watan Agustan wannan shekarar inda
kuma yace malamin na samun damar hakan
ne a duk lokacin da yazo yi masu karatun
harshen Larabci a gidan su.

NAIJ.com ta samu cewa shi kuma a nasa
bangaren tuni malamin na Islamiya ya
karyata wannan zargin da ake yi masa Inda
kuma ya nemi tsarin Allah daga aikata dukkan alfasha.

Alkalin kotun Taiwo Akanni ya bada belin
malamin kan Naira 250,000 tare da shaidu
biyu wanda malamin zai kawo sannan ya
daga shari’ar zuwa 11 ga watan Satumba.
No comments:
Write Comments