Friday

Home BUHARI YAYIWA GWAMNAN JIHAR OSUN WAYA.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kira wo gwamnan jihar Osun Rauf Aregbesola ta wayar tarho inda ya yi masa ta'aziyyar rasuwar mahaifiyarsa Saratu Aregbesola.Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Mallam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twiiter ta ce Shugaba Buhari, wanda ya kwashe sama da wata biyu yana jinya a London, ya yi wayar ne ranar Alhamis.
Ya kara da cewa shugaban ya yi addu'ar Allah ya jikan Saratu Aregbesola.
A cewar sanarwar, shugaban na Najeriya ya bayyana marigayiyar a matsayin "mace mai kwazo wacce ta kasance katanga ga 'ya'yanta.''
A watan jiya ma, Shugaba Buhari ya yi wa tsohon shugaban jam'iyyar APC mai mulkin kasar Cif Bisi Akande wayar tarho, inda ya yi masa ta'aziyya a kan rasuwar matarsa Madam Omowunmi Akande.
No comments:
Write Comments