Tuesday

Home Dandalin Kannywood: Ba zan taba auren dan fim ba - Nafisa Abdullahi
Shahararriyar yar wasan Hausa din nan a
masana'antar fina-finai ta Kannywood watau Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa ita ba zata auri dan fim ba ko wanene don tana da masoya da dama kuma a ciki ma har ta fitar da wanda take so.

Jarumar tayi wannan ikirarin ne a cikin
wata fira da tayi da majiyar mu yayin da take amsa tambayoyi daga wakilin na majiyar.

NAIJ.com ta samu cewa da aka tambaye ta
kuma ko me gaskiyar labarin cewa an sa
mata biki amma sai ka kuma fasa, sai
jarumar ta kada baki tace ita dai a iya sanin ta ba ta san da wannan maganar ba amma watakila masu maganar su ne suka sa mata bikin.

Ta ci gaba da cewa ita dai abun da ta sanishine ta na masoya da dama kuma ita tun tuni ta fitar da wanda take so kuma shi zataaura cikin izinin Allah a nan gaba kadankuma ta kara da cewa shi din ba dan fim bane.

Ku kalli wannan.
No comments:
Write Comments