Wednesday

Home Fina-finan Kannywood da ya kamata ku kalla a wannan watan

Watan Agusta ya zo da ruwan fina finai masu kayatarwa, daga masana'antar shirya finan finan hausa da a ke kira "Kannywood", da masu kallo ya kamata su nema don nishadin su.

1. MATATA CE SHAIDA

Labari ne na wani magidanci da ke fuskantartuhuma a gaban bisa zargin aikata laifin kisan kai, magidancin ya kasance bashi da wata shaida da zai gabatar domin gamsar da kotu a kan ba shi ya aikata laifin basai matarsa, hujja da a yawan lokuta kotu bata karba. Shin ko kotu za ta yi amfani da matar sa a matsayin shaida domin wanke shi daga zargin aikata laifin kisan kai?.

2. Karamci:

Shiri ne da yake nuna halayyar wasu iyaye
wajen yi wa 'ya'yan su zabin abokin zaman
aure.

3. Yar' Duniya:

Labarin wata tsintacciyar yarinya ce da wasu
ma'aurata suka dauko daga gidan raino
saboda basu samu haihuwa ba. Yarinyar ta
taso cikin wadata da jin dadi, saidai bayan
girmanta halayenta sun munana, sun saba da
irin tarbiyyar da iyayen rikon nata suka
bata.
Hausa Naij.com

4. Mijin yarinya:

Shirin yana nuni kan halin kunci da takura
da 'yan mata masu karancin shekaru ke
fuskanta wurin manyan 'ya'yan kishiyoyi
yayin da aure ya kai su gidan yawa.

5. Mansoor:

Shirin Ali Nuhu da tuni a ka nuna shi a
manyan sanimomi tun karamar sallah.
Labari ne da yake nuna halin tsangwama da
kyama da yaran da a ka haifa babu aure ke
fuskanta a rayuwa duk da kasancewar ba su
suka zabi zuwa duniya ta wannan hanya ba.
No comments:
Write Comments