Tuesday

Home Gwamnatin tarayya ta ba da hutun kwanaki 2 don bikin Sallah
Ministan cikin gida, Abdulrahman Danbazau ya sanar da ranaku biyu a matsayin ranakun hutun Sallah babba.

- Danbazau ya bukaci yan Najeriya da suyi
amfani da ranakun biyu, 1 ga watan Satumba da
4 ga wata don yiwa kasa addu’an samun zaman lafiya
- Ya kuma gargadi yan kasa masu kalaman
batanci da su guje ma haka domin gwamnati
bazat lamunta ba.

Gwamantin Tarayya ta amince da ranakun
Juma’a, 1 ga watan Satumba da kuma Litinin, 4 ga watan Satumba, a matsayin ranakun hutun Sallah Babba.

Ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau
ne sanar da haka, a madadin gwamnatin
tarayya, inda ya ke taya daukacin al’umman musulmai da ‘yan Najeriya baki daya murna.

Ya kuma yi addu’ar gudanar da shagulgulan
sallah lafiya, tare da samun zaman lafiya da hadin kan kasar nan.
Danbazau ya bukaci yan Najeriya da suyi
amfani da ranakun biyu, 1 ga watan Satumba da 4 ga wata don yiwa kasa addu’ar samun zaman lafiya.

Gwamnatin tarayya ta ba da hutun kwanaki 2 don bikin Sallah.

Ya kuma tabbatar dasamun zaman lafiya tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, ya na mai umartar jami’an tsaro su tabbatar da wanzuwar hakan.

Ministan ya yi tir da munanan kalaman
kiyayya ya na mai gargadin masu zuguguta
kalaman su kuka da kan su.
No comments:
Write Comments