Saturday

Home › › Halin da Amurka ta jefa duniya a ciki {katanta kaji bayani malam}
Bayan yakin duniya na biyu an dora duniya a kan yarjejeniyar Yalta, amma sai ga shi tun kafin a yi rabin karni da samar da wannan abu ya lalace. A yanzu ana neman sake kara wa’adin wannan abu amma kuma sakamakonsa miliyoyin mutane na ci gaba da mutuwa.Bayan yakin duniya na biyu an dora duniya a kan yarjejeniyar Yalta, amma sai ga shi tun kafin a yi rabin karni da samar da wannan abu ya lalace. A yanzu ana neman sake kara wa’adin wannan abu amma kuma sakamakonsa miliyoyin mutane na ci gaba da mutuwa.

Tsarin duniya da aka kafa a shekarar 1945 a Yalta yakawo karshe a shekarar 1991 wanda shugaban daular Soviet Mihail Gorbaçov ne ya kawo karshen ta. Shin ya aka ba da dewa ba wannan abu ya lalace, kuma sai ga shi an zo an samar da kasashe 5 da su kadai ne suka isa su yanke hukunci a zauren Majalisar Dinkin Duniya.
Duk da cewa Rasha na daya daga cikin wadannan kasashe 5 amma kuma ahakan ya zama abu da ya ci karo da manufofin Perestroika.

Tare da Perestroika ne wannan daula ta fadi inda tattalin arzikinta dk zama daya daga cikin kasashe 5 mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Daga nan sai Amurka ta zama ita ce jagorar sabon tsarin da aka dora duniya a kai. Idan haka ne Amurka sai ta zama daula mai shekaru 200. Amma kuma abin takaici ba ta da ajin masu hannu da shuni. Domin idan ana so a kafa wannan aji to za a dauki shekaru 400.

Amurka kasa ce da ba ta da ajin amsu hannu da shuni, kuma ta samu daga mutane da suka dinga yin hijira daga kauyuka zuwa birane nda sukadinga bin hanyoyi da ba sa bisa ka’ida wajen gina kasar tare da habaka ta.

A kokarin da aka yi aiwatar da wannan sabon tsari akn al’uma sai da wasu mutane suka dauki alkalami suka yi rubutu misalinsu shi ne, Fukuyama da Huntington.

Sai da aka yi aikin juya tunanin mtane domin cin nasarar wannan manufa. A karshe dai a lokacin Bush na farko sai da aka mayar da wannan manufa ta koma ta yaki. An amince cewa, yarjejeniyar Yalta ta shekarar 1945 ce ta haifar da yadda Baba Bush ya afkawa Iraki da sunan yakin ukuntaka a Gabas ta Tsakiya.

Asali dai, tun daga Magna carter da kuma yadda al’adun Turai suka dinga sauyawa, George Herbert Walker Bush ya afkawa Iraki a shekarar 1991 inda ya kuma furta cewa, yana yin yaki amadadin imanin ukunta ka ne.

A wancan lokacin, tunanin Turai na iya fitar da wani amo. Amsu son cigaba, marubuta, al’umar jami’o’i, da sauran jama’a sun dinga kuwwa tare da nuna ba su amince da wannan mamaya da Amurka ta yi wa Iraki ba. Misal shi ne, Malamin Falsafa na Spaniya Santiago Alba Rico ya yi rubutu wanda ya kusa zama wani kakagida ga manufofin duniya a wancan lokacin. Rico sai da ta kai matakin da abin da ya rubuta ya kira wannan manufa da cewa “Wani fashi da makami ne da kasashen yamma suke wa sauran kasashen duniya kanana baki daya.”

Hakikanin gaskiya, bayan an rusa daular kwamunisanci, abun mamaki ne yadda yankunan da suka sha fama da yake-yake da rikici sai ga shi sun zama manyan cibiyoyin kasuwanci da kuma matattarar makamashi. Sai kuma hi tun daga Afganista har zuwa Aljeriya ana ta samun fitar kungiyoyin ta’adda.

Jaridar Independent ta fitar da wani şlabari a shafinta na farko da shafi na 10 inda ta bayar da sanarwa game da hakan. A labarin da jaridar ta yi ta ce, Osama da jama’arsa na kan hanyar samar da zaman lafiya. Kuma ana nuna Bin laden a matsayin mara alaka da ‘yan ta’adda. Kamar dai yada a shekarun1980 aka dinga nuna Saddam Hussain a matsayin wani bardeko jarumi a lokacinda ya ke kai wa Iran hari.
Bayan wani dan lokaci sai kuma kasashen Turai suka fara kiran wannan mutum da suka kira a baya mai girma da cewa dan ta’adda ne. A karshe dai sai da Baba Bush suka mamayi yankinmu da wuta.

A wadannan shekaru ne dai wata kungiya ta ta’adda mai zubar da jini da ake kira FIS ta bulla. Kuma kungiyar ta kare aka neme ta aka rasa a lokacinda Amurka da kamfanunnukan Aljeriya suka amince cinikayyar makamashi.

Dukkanin shugabannin Amurka da suka z oba su iya tsinana wani abu ba na samar da dabi’ar ajin masu hannu da shuni a kasar ba, sai ma suka rungumi dabi’ar masu mülkin mallaka.

Amurka ta janyowa dukkan dan adam matsala sosai ta hanyar runguma tare da dabbka manufar “New World Order” wato sabuwar manufar duniya kuma a kan tsari na zalunci da rashin adalci. Kuma Amurka ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin wannan tsari nata na rashin adalci. Masu da’awar ‘yancin demokradiyya sun dinga yada manufarsu ta boye, amma kuma ‘yan Republicans na nuna kyamar hakan.

Kuma wadanda wannan tsari ya reno tare tarairaywa, sun dinga amfanida munanan halaye da rashin tarbiyya da ma zalunci don ganin tsarin ya ci gaba. Hakan ne ya sanya shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya ke cewa, “wannan ta’addanci da kuke raino wata rana zai dawo zuwa gare ku. Kuma abin takaici a yau wannan matsala ta zama ta duniya baki daya. Kuma abin ya fi karfin Tura a yanzu. Amma duk da haka wannan tsari na zalunci na manufofin sabuwar duniya na ci gaba da tafiya wanda kuma shi ne ya ke kara haifar da ta’addancin.

Tun daga al’umar AMurka da na kasashen Yamma, kowa ya tsaya yana kallon shirn sabon shugaban kasar Amrka Donald Trump zai ci gaba da aiwatar da wannan tsari ko kuwa a a.

Amma abin da muke gani a yanzu shi ne Trump ya damu da wannan abu kuma ba ya son sa. Muna fatanabin da Erdoğa ya ke fada tsawpn lokaci ne zai faru wato duniya ta samu shugaba na adalci.
Karshen shirin na wannan lokaci kenan sai mu hadu a makomai zuwa don jin wani sabon shirin daga nan TRT hausa Muryar Turkiyya.
No comments:
Write Comments