Wednesday

Home Jahohi 3 da aka gabatar da gagarumin buki saboda dawowar buhari.
- Jihohin Arewa sun yi biki dalilin dawowar Buhari - Irin su Jihar Kogi dai har hutu aka bada na musamman - A Jihar Kaduna ma an shirya wani kasaitaccen biki.
Labari ya zo mana cewa wasu Jihohi sun shirya biki na musamman dalilin dawowar Shugaba Buhari bayan jinyar rashin lafiya. Daga Jihohin da su kayi biki akwai: An shirya biki don dawowar Buhari.
1. Jihar Kogi: Irin su Jihar Kogi dai har hutu aka bada na musamman saboda dawowar Shugaban kasar. Jama'a dai sun soki hakan amma Gwamnan Jihar yayi kokarin kare kan sa. 2.Jihar Kaduna: A Jihar Kaduna nan ma mai ba Gwamnan Jihar shawara kan harkokin siyasa watau Uba Sani ya shirya biki na musamman duk a dalilin dawowar Shugaban kasa Buhari. GA VIDEON WANDA AKAYI A KADUNA


 3.Jihar Katsina : Mu na da labari cewa mai girma Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari da wasu 'Yan Jihar sa sun yi wani zagaye saboda murnar dawowar Shugaban kasar. <!-- AdSense --!>

 A halin yanzu dai Jama'a da dama na cike da farin ciki a dalilin dawowar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
No comments:
Write Comments