Friday

Home › › Jami'an hukumar kwastam sun damke mawakinnan rarara.
Labarin da ke zuwa mana yana nuni ne da cewa ma'aikatan hukumar nan da ke sa ido ga harkokin shige da fice ta tarayyar Najeriya karkashin shugabancin Kanal Hamid Ali ta kama motoci mallakin mawakin nan na Buhari watau Rarara.


Shahararren mawakin Buhari, Rarara ya shiga hannun jami'an Kwastam
Jami'an hukumar sun kama motocin ne da ake kyautata zaton na mawakin ne da ya shigo da su ta barauniyar hanyoyin da kasar Najeriyar ta haramta shigowa da su na kan iyakokin kasar Nigar da Benin.

NAIJ.com dai ta sumu daga majiyar ta cewa an dai kama manyan motocin na shi ne kirar fijo-fijo da toyota-toyota a jihohin Zamfara da Sakwato kuma aka kawo su Kaduna.

Tuni dai yan Najeriya da dama suka fara tofa albarkacin bakin su game da lamarin inda suka zuba ido su ga ko za'a yi masa hukunci dai dai da kowa ko kuwa za'a yi son kai a saki motocin nasa.
No comments:
Write Comments