Wednesday

Home Jami'an tsaro sun harbe wani mutum a fili a kan ya yiwa 'yar shekara 3 fyade: (karanta)
Kalli sauran hotuna.


A can kasar Yemen ne a ka gurfanar da wani mutum da laifin yi wa 'yar shekara 3 fyade sannan kuma ya kashe ta wanda hakan ya sa a ka harbe shi a fili don ya zama izina ga jama'a.A ranar litinin din da ta gabata ne cikin garin Sanaa da ke kasar Yemen, daruruwan jama'a su ka yi cincirundo don ganin yadda za a harbe wani mutum saboda ya yiwa 'yar shekara 3 fyade kuma ya kashe ta.


An harbe Muhammad Al-Maghrabi mai shekaru 41 a duniya da bindiga kirar Ak47 a
tsakiyar garin Sanaa inda daruruwan jama'a su ka fito kallo.


Muhammad Al-Maghrabi kafin a harbe shi.


Motar 'yan sandan da ta dauko Muhammad zuwa tsakiyar garin Sanaa mai suna Tahrir ta samu rakiyar wasu motocin na 'yan sanda har guda biyar saboda gudun ko ta kwana
don ganin irin yawan jama'ar da su ka fito ganin zartar da hukuncin.
No comments:
Write Comments