Thursday

Home Jami'an "Yan Sanda na neman wani malami ruwa a jallo sakamakon ta'asa dayayi akan wata gawa.
zuwa yanxu dai mutanen unguwar sun suburbudi mahaifin malamin.


Hukumar Yansandan jihar Kwara ta dukufa wajen neman wani malamin addinin Musulunci wanda
ake zargi da hakar kabarin abokinsa don yin tsafi da gawar tasa, inji rahoton kamfanin dillancin
labaru, NAN.Wannan Malami da ake nema, a cewar Yansanda, mazaunin unguwar Oloje ne, kuma ya hako kabarin abokin nasa ne bayan kwanaki bakwai da mutuwarsa a ranar Talata 1 ga
watan Agusta.

Makwabtan wannan Malami ne suka kai kararsa ga Yansanda bayan wani mugun wari ya
ishe su a gidajensu, inda suka fara bin diddigin daga ina warin ya fito, har suke iske silan
warin a dakin Malamin, nan fa suka tarar da gawar abokinsa, Sulaiman.

Jin makwabtan na bidar daga inda warin ke fitowa ya sanya Malamin tserewa, Marigayi
Sulaiman ya rasu ne a ranar Alhamis din data gabata, jim kadan bayan sun fita tare da
Malamin, tunda dama an tabbatar amininsa ne tun suna yara, inji majiyar NAIJ.com .

Sai dai cikin fushi, makwabtan suka jibgi maihaifin Malamin, sa’annan suka rusa gidan su gaba daya inda suka gano sassan jikin mutum a gidan. daga karshe Kaakakin yansandan jihar DSP Ajayi Okasanmi yace suna gudanar da bincike.
No comments:
Write Comments