Friday

Home KALUBALEN DA RAGEN MAKIN DA HUKUMAR SHIRYA JARABAWAR JAMB TAYI DAGA 180 ZUWA 120 ZAI JAWO A KASAR NAN.
KALUBALEN DA RAGEN MAKIN DA HUKUMAR SHIRYA JARABAWAR JAMB TAYI DAGA 180 ZUWA 120 ZAI JAWO A KASAR NAN.

Ya'yan Talakawa zasu sha wahala.

Hukumar Jarabawar sharar fagen shiga Jami'a Jamb ta rage adadin makin jiga Jami'a daga makin Dari da Tamanin 180 zuwa Dari da Shirin 120.
Hukumomi Jami'oi tare da hadin Gwiwar hukumar shirya jarabawar sharar fagen shiga Jami'a Jamb su suka yanke hukuncin bayan wata tattaunawa ta musamman data gabata a ranar Talatar.

Sai dai wasu daga cikin Dalubai sun kalubalanci batun da cewar rage makin zai iya haifar da Matsala a tsakanin Ya'yan Talakawa saboda idan har dan gidan Talaka yaci 230 za'a iya hana shi Admission a baiwa Dan gidan mai Kudi daya samu sakamakon 120 wanda hakan kwatakwata bai dace ba.

Wani matashi mai suna Umar Umar yace maganar gaskiya ba wai yana bakin ciki da yadda aka rage makin bane, a'a matakan da za'a bi wajen bayar da Admission din shine zai baiwa wanda bashi da Uwa a gindin murhu wahala.

Akwai da yawa wadanda suka sami maki sama da Dari da chasa'in 190 zuwa Dari biyu 200 kuma baza su sami damar shiga makaranta ba saboda basu da kowa, amma wadanda suke da maki 120 masu daurin Gindi zasu sami damar shiga Jami'a.
To allah dai yabamu sa'a
No comments:
Write Comments