Thursday

Home Kungiyar Boko Haram ta kashe mutane 3, ta sace wasu 3 a Yammacin jiya Laraba


An kawo gawawwakin wasu 'yan uwan 2 da
wani mutum da ake zargi da cewa Boko
Haram ne suka kashe su kusa da kauyen
Molai yayin da suka yi garkuwa da wasu 3 a unguwar Silimari da ke Maiduguri babban
birnin jihar Borno a yammacin ranar
Laraba, 16 ga watan Agusta.

A cewar ‘yan farautar kauyen wanda
Ahmadu Tukur ya jagoranta, ya ce 'yan
kungiyar Boko Haram sun kashe daya daga
cikin abokan aikinsu a wannan rana, kuma
suka sace wasu kananan yara kimanin
kilomita daga kauyen Molai.

Kamar yadda NAIJ.com ta samu labari, Tukur yace: "Mun samu labari cewa wasu yara sun tafi gona a kusa da inda gwamnatin tarayya ke ajiye kayan abinci yayin da ba su dawo gidaba”.

"Mun shirya kuma muka ci gaba da nemo
yaran kawai muka gano gawawwakinsu inda
aka daure hannayensu a baya kuma
kawunansu duka sun yanke su kuma sun
sanya musu a baya”, inji shugaban ‘yan
farautan.

Tukur ya ci gaba da cewa: “Wannan shi ne
irin yadda Boko Haram ke aikata ta’addanci.

Gawan mutumin na uku ba mu da labari da
shi, amma mun kawo gawawwaki uku zuwa
gidan Bulama a unguwar Silimri”.
No comments:
Write Comments