Saturday

Home LABARI DA DUMI DUMI Ayau Buhari Zai Dawo Gida NageriyaDaren yau Asabar ko gobe Lahadi Shugaban kasa Muhammad Buhari zai dawo nan gida Najeriya, a ranar Litinin kuma ya shiga ofishin shi ya kama aiki.

Wani na kusa da Shugaban kasa Muhammad Buhari shiya bayyanawa wakilin mu Shuaibu Abdullahi a wata zantawa da suka yi ta wayar tarho a daren jiya Juma'a.
Na kusa da Shugaban ya bayyana cewar ko shakka babu shugaban kasa Muhammad Buhari ba zai wuce yau Asabar ko gobe Lahadi ba, kuma ranar litinin ya shiga ofishi ya kama aiki.

Jaridar Dimokaradiyya ta ruwaito cewar duk da dai na kusa da shugaban bai bayyana mana dai dai lokacin da shugaban zai sauka ba, amma ya tabbatar mana da cewar yau ko gobe zai dawo kuma a babban birnin tarayya Abuja zai sauka.
Allah ya dawo dashi lafiya.
Daga Jaridar Dimokuradiyya
No comments:
Write Comments