Sunday

Home Manyan Matakan da Shugaba Buhari ka iya dauka a gobe Litinin .
- A gobe Shugaba Buhari zai yi wa 'Yan Najeriya
jawabi
- Jama'ar kasar sun tasa kunne ana jiran lokacinyayi.Kun dai ji cewa ana dai jira zuwa gobe
domin jin abin da Shugaban kasar zai fara dashi.

A jiya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya
dawo gida bayan ya dauki sama da kwana
100 yana jinya a Landan. Kowa dai yana jira domin jin abin sa Shugaban kasar zai fada a Safiyar Litinin.

Shugaba Buhari zai yi jawabi a Gobe Litinin.

1.Murabus daga mulki
Wasu na gani cewa Shugaban kasar zai iya
sauka daga mulki ko da a taba yi ba a
Najeriya. Ba shakka Shugaba kasar ya aminta da rikon Mukaddashin nasa Farfesa Yemi Osinbajo amma hakan da wuya ganin yadda Shugaban kasar ya murmure.

2.Sauya mukaman Gwamnati
Ku na da labari Jama'a sun fara maganar
sauke wasu Ministocin kasar. Wasu na tunani zuwa Ranar Litinin a dauki wannan mataki. Hakan dai ba zai zo da mamaki ba.

3.Cire Hafsun Sojin kasar
Dama dai wa'adin Shugaban Hafsun Sojin
Najeriya Abayomi Olonisakin ya cika kafin a kara masa.

Bayan tafiyar Shugaba Buhari
Boko Haram ta dawo da karfi ko hakan zai sa a dauki wani matakin?.

Tun a jiyan dai Shugaban kasar ya gana da Manyan Sojojin kasar.
No comments:
Write Comments