Tuesday

Home › › Martanin shugaba buhari zuwa ga masu zanga-zangar ‘ka Dawo kokayi Murabus' a kansa - Adesina.


Maiba shugaban kasa Muhammadu Buhari
shawara na musamman a kafofin zumunta da
watsa labarai, Femi Adesina, ya bayyana
abunda ya gani game da shugaban kasar a
lokacin da ya bi sahun wasu tawaga zuwa
Landan kwanan nan.

Adesina ya tabbatar da cewa lallai shugaban kasar na cikin kosin lafiya sannan kuma ya nuna cewa lallai ya shirya tafiyar saóí shidda don dawowa Najeriya.

Da yake Magana a lokacin wani shiri na
Channels TV a ranar Litinin, 14 ga watan
Agusta, Adesina ya kuma bayyana cewa masu
bukatar shugaban kasa ya dawo tare da
likitocin sa maimakon ya tsaya a Landan
suna dai nuna ra’ayinsu ne kawai.


Ya ce shugaban kasar ya fada masu yana
bibiyar abubuwa tun bayan barinsa kasar a
ranar 7 ga watan Mayu.

A cewarsa, Buhari ya kuma yi Magana game
da zanga-zangar da wata kungiya ke yi a
yanzu inda suka bakaci da ya yi murabus.
Yace a tunanin shugaban kasar zanga-zangar na cikin yancin damokradiya cewa masu zanga-zangar na gudanar da yancin su ne.

Ya kuma bayyana cewa gaskiya bai san
wadanda ke daukar nauyin maganin Buhari
ba a Landan.

Ya kuma yi bayanin cewa zaá ga kokarin
shugaba Buhari sosai kafin wa’adin mulkinsayakare a 2019.
No comments:
Write Comments