Tuesday

Home Na kwashe Iyalai na kaf daga sansanin ‘yan gudun hijra saboda fyade da ake wa mata
Mutane sama da miliyan biyu ne suke zaune a sansanoni daban- daban dake jihar Borno
sakamakon rikicin Boko Haram da ya raba su da muhallinsu.

A maimakon su samu tsaro da kwanciyar
hankali a sansanonin sai gashi hakan ya
faskara sakamakon yawan fyade da akeyi ga
mata a ko wani dare.

Daya daga cikin yan gudun hijira dake a
sansanin Dalori mai suna Baba Kura mai
shekara 67 a duniya ya ce yayi kaura da
iyalansa daga sansanin wannan mummunan
abu da ake aikata wa mata ta karfin tuwo.

A cewarsa: ‘‘Ina da‘ya’ya mata shida;uku
daga cikinsu zaurawa ne sauran ‘yan mata.
Kusan kowani dare za kaji ihun mata ana
musu fyade a sansanin Dalori wanda hakan ya sa nake gadin ‘ya’yana kowani dare.”

Baba kura ya ce dole yayi kaura daga
sansanin.

Wata mazauniyar sansanin ta ce Allah ya
kubuta da ita daga harin da aka kai don yi mata fyade lokacin da wasu matasa suka
kawo mata dauki bayan an bita da gudun
tsiya za a danne.

Ta ce garin wannan gudu ne ta fadi har ta
Karya kafadarta.
No comments:
Write Comments