Friday

Home Osinbajo ya gana da wakilan gamayyar kungiyar yan Niger DeltaAn gana ciken daren jiya tsakanin mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo da wakilan gamayyar kungiyar kare muradun ‘yan yankin Niger Delta, wadanda a cikin watan nuwambar bara suka bukaci gwamnati ta biya wa ‘yan asalin yankin wasu bukatu 16 ko kuma su janye gudunmuwar da suka bayar domin samar da tsaro a yankin mai arzikin mai.

Wasu daga cikin mahalarta wannan taro sun hada da ministan raya yankin Niger Delta, da kuma wasu tsoffin gwamnoni da ake kallo a matsayin dattawan yankin.

Gwamnatin Najeriya na kokarin kawo karshen rikicin yankin da yanzu haka ta janyo asarar rayukan jama’a.
No comments:
Write Comments