Monday

Home Osinbanjo ya janye sunan mutanen da ake zargi da Rashawa.
Duba jerin sunayen.

prof Yemi Osinbajo

Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbanjo ya janye suna wasu mutane biyu da aka nada a hukumar gudanarwar hukumar yaki da almundahana ta ICPC saboda zargin da ake musu na cin hanci da rashawa.

Mai taimakawa shugaban Laolu Akande ya ce an janye sunan Maimuna Aliyu da Sa’ad Alanamu daga cikin sunayen da Osibanjo ya bayyana a matsayin hukumar gudanarwar.

Ana tuhumnar Alanamu ne kan zargin cin hanci lokacin da ya rike mukamin shugaban hukumar kula da ilimi mai zurfi a Kwara, yayin da ita kuma Maimuna Aliyu ake zargin ta karya ka’idar aiki da karkata kudaden talakawa lokacin da take aiki a asusun ajiyar Aso Savings.

Nadin mutanen biyu ya gamu da suka daga sassan Najeriya saboda tuhumar da ake musu.
No comments:
Write Comments