Friday

Home Rikita-Rikita: An bindige mutane 2 har lahira yayin da kazamin rikici ya barke a sakatariyar APC

Ya zuwa yanzu an samu tabbacin mutuwar
mutane biyu yayin da kuma da yawa suka jikkata bayan da wani kazamin rikici ya barke a tsakanin magoya bayan jam'iyya mai mulki ta APC a sakatariyar ta a jihar Bayelsa.

Bayanan farko-farko da muka samu sun
bayyana cewa wasu en bindiga dadi ne da
ba'a san ko suwaye ba suka doshi sakatariyar suna ta harbe-harbe a dai-dai lokacin da ake rantsar da sabon shugaban jam'iyyar na rikon kwarya a jihar mai suna Mista Joseph Fafi.
hausa naij.com
NAIJ.com har ila yau ta samu cewa daya daga cikin wadanda suka rasa ransu dan siyasa ne kuma dan jam'iyyar ta APC daga karamar hukumar Sagbama sai kuma dayan wani mai talla ne da ya zu wurin kuma dukkanin su sun gamu da ajalin su ne sakamakon harben bindiga.

Haka ma dai yanzu haka an bayyana cewa
mutane da yawa da ba'a san adadin su ba
suna a asibiti suna karbar magani
sanadiyyar munanan raunukan da suka samu
lokacin da ake yin turmutsutsun.
No comments:
Write Comments