Wednesday

Home Wani jami'in EFCC ya kubuta a hannun 'yan bindiga.

Wani babban jami'in Hukumar hana yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta'annati, EFCC ya tsallake rijiya da baya a yayin da wasu 'yan bindiga suka bude masa wuta a birnin Port Harcourt na jihar Rivers.

Mista Austin Okwor, wanda jami'i ne ofishin EFCC a Port Harcourt, ya bar ofishin hukumar bayan ya tashi aiki a lokacin da wasu 'yan bindiga suka bude masa wuta. Ya yi sa'ar tsere wa maharan amma sai da ya sami raunuka domin sun cigaba da harbinsa.

Babban jami'in shiyyar Port Harcourt na hukumar EFCC ya ce an riga an shaida wa 'yan sanda wannan lamarin.
Mista Okwor na cikin jami'an da ke binciken batutuwan da suka shafi wasu alkalai.

Kafin wannan harin, jami'in ya sha samun sakonnin barazana. An sanar da 'yan sanda sako na baya-bayan nan da ya samu a watan Mayun bana.

Idan ba a manta ba, a watan Satumba na 2014 aka kashe jami'in hukumar mai kula da sashin bincike, Abdullahi Mu'azu a Kaduna. Watanni shida kafin wannan lamarin an kai wani harin a kan motar dake dauke da wasu jami'an hukumar masu shigar da kara a wata kotu a birnin Owerri na jihar Imo.

A sanadiyyar harin aka kashe Sajent Eze Edoga kuma aka raunata Joseph Uzor, babban lauyan hukumar.
No comments:
Write Comments