Saturday

Home › › Yara 64 sun mutu a asibitin gwamnatin India acikin kwanaki 6{karanta}

Wasu jami'ai na duba tukwanan iskar da mara lafiya ke shaka a asibitin Baba Raghav Das da jihar Uttar Pradesh AFP.

Akalla kananan yara 64 sun rasa rayukansu a cikin kwanaki shida a wani asibitin gwamnati da ke yankin arewacin India sakamakon karancin na’urar taimaka wa mara lafiya yin numfashi.

Tuni hukumomin kasar suka kaddamar da bincike kan musabbabin karancin na’urorin a asibitin na Baba Raghav Das da ke garin Gorakhpur na jihar Uttar Pradesh.

Wasu rahotannin na cewa, an samu karancin na’urorin shakar iskar ne saboda bashin kudi da kamfanin samar da na’urorin ke bin asibitin.

Sai dai karamin ministan kiwon lafiya na kasar, Sidharth Nath Singh ya musanta cewa, mutuwar yaran na da nasaba da karancin na’urorin.
No comments:
Write Comments