Sunday

Home › › Zaben kasar kenya yabar baya da kura. An samu salwantar rayuka.
Birtaniya a jiya asabar ta aike da sakon taya murna ga Uhuru Kenyatta bayan nasarar da ya samu a zaben kasar.

Birtaniya ta jaddada goyan bayan tareda ci gaba da huldar diflomasiya da Kenya kamar dai yadda Ministan harakokin wajen Birtaniya Borris Johnson ya sanar.

A daya wajen an share daren jiya yan Sanda na fuskantar boren masu zanga-zanga a wasu unguwanin birnin Nairobie.
Tawo mu gama da ta yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 100 a cewar yan adawa, yayinda bangaren hukuma suka bayyana mutuwar mutane kusan 20.


Tun bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da sakamakon zaben , Raila Odinga ya karaucewa manema labarai ba tareda ya yi jawabi a kai ba.

Wasu kungiyoyin kasar sun nuna matukar kaduwa ganin ta yada yan sanda ke amfani da karfi da ya wucce kima wajen tarwatsa masu zanga-zanga.
No comments:
Write Comments