Saturday

Home An kashe manyan kwamadojojin Boko Haram a Najeriya wani hari ta sama. :sunayensu

Rundunar Sojin Najeriya ta Bayyana cewa, ta kashe wasu manyan kwamandojin kungiyar ta’adda ta Boko Haram su 5 a wani hari ta sama da suka kai musu a jihar Borno da ke arewa maso-gabashin kasar.

Rundunar Sojin Najeriya ta Bayyana cewa, ta kashe wasu manyan kwamandojin kungiyar ta’adda ta Boko Haram su 5 a wani hari ta sama da suka kai musu a jihar Borno da ke arewa maso-gabashin kasar.
Kakakin sojin kasar Birgediya Janar Sani Kuma Usman Sheka ya sanar da cewa, kwamandojin na Boko Haram da aka kashe sun hada da Abu Dujana; Man Tahiru, Man Chari; Malam Abdullahi Abu Sa'ad da Goni Bamanga.
Wani faifan bidiyo da aka raba wa manema labarai wnda ya nuna yadda aka kai harin ya tabbatar da nasarar da aka samu.

Rundunar Sojin Najeriya dai na yaki da ‘yan ta’addar na Boko Haram tun shekarar 2009.
No comments:
Write Comments