Tuesday

Home An Kirkiro Manhajar Komfutar Hausa Da Ba Irinta A Duniya
Najeriya, an kaddamar da wata manhaja mai suna Rumbun Ilimi, wadda ke kunshe da bayanai a kan fannonin rayuwa da fagen ilimi daban-daban cikin harshen Hausa zalla.
An kwashe shekara tara ana tsara manhajar kamar yadda wanda ya kirkiro ta ya bayyana a lokacin kaddamamarwar.
Mallam Abubakar Muhammad Tsangarwa, shi ne ya kirkiro manhajar, kuma ya shaida wa BBC cewa, manhajar ta kunshi darussa a bangarori na rayuwa daban-daban a cikin harshen Hausa.
Malamin ya ce a yanzu akwai lambar da ake kira idan ana so a samu manhajar, wadda ita ce 08039648244, ga duk wanda yake bukata, ko da yake ya ce a yanzu suna kokarin yin ‘yan gyararraki a kai, kafin nan da ‘yan kwanki masu zuwa su kammala..
No comments:
Write Comments