Monday

Home › › “Buhari ya bar Nigeria, wannan da kuke gani daga sudan akayo hayar shi”:Nnamdi kanu

Sahara reporters ta ruwaito cewa, shugaban 'yan asalin yankin Biyafara, Nnamdi Kanu, ya bayar da tabbacin cewa, wanda yake mulkar Najeriya a yanzu haka ba shugaba Buhari ba ne, domin kuwa gwamnatin Najeriya ta dauka hayar wani ne mai kira dakuma zubi irin na Buhari wajen ci gaba da mulkar kasar nan.

A kalamansa, "Mutumin da kuke kallo a
gidajen talabijin ba Buhari ba ne, daga kasar Sudan yake. Bayan aiki na tiyata da
kwararrun likitoci suka gudanar shine aka
kawo shi kasar nan. An koya wa mutumin
halayya da kuma dabi'u irin na Buhari saboda haka kar ya rude ku. Zan iya tsayawa kuma in tabbatar da ko ni waye, amma Buhari ba zai iya yin haka ba, domin haka ba zai iya yaudarar Nnamdi Kanu da IPOB ba,"
in ji shugaban IPOB.

Kanu ya bayyana cewa, babban kuskuren da
Buhari ya yi a baya shine, daurin da sanya aka yi masa, sanadiyar bayyana ra'ayin shi da kuma shugabancin 'yan asalin yankin Biyafara a kan fafutukar neman yankin su.

Shugaban na IPOB ya yi tir da kamfanin
jaridar THE SUN, bisa wallafa labarun karya da suka shafe shi, da cewar wai ya arce.
Ya kara da cewa, ba shi da ra'ayin yin wani furuci, amma yanzu ya zamto tilasa ne a agare shi sanadiyar karairayi da gidajen jaridu suka wallafawa akansa don kawai jaridar su ta samu shiga a kasuwa.

Ya kuma shawarci magoya bayansa akan yin
watsi da duk wani abu da suka gani ko kuma suka saurara daga kafofn watsa labarai, face abin ya zo daga gare shi ne.
No comments:
Write Comments